Ɗan takara a jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya taya Bola Ahmed Tinubu, murnar nasara a zaɓen fitar da gwani na APC.
Atiku ya ce zaɓen ya kasance wanda aka fafata sosai, sai dai nasarar Tinubu na sake tabbatar da jajircewarsa.
Sannan ya kara da cewa ana iya boye abubuwa da dama, sai dai batun gazawar gwamnatin APC ba abin da zai ɓoyu ba ne.
Sannan Atiku ya ce, zaben 2023 zai kasance wani kuri’ar jin ra’ayi kan gazawar da gwamnatin APC ta nuna a mulkinta.