Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, a ranar Litinin ya gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a Abuja, kamar yadda jaridar PUNCH ta rawaito..
Atiku ya doke Wike ne a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja a daren ranar Asabar.
Atiku ya samu kuri’un wakilai 371 yayin da abokin hamayyarsa (Wike), ya samu kuri’u 237.
Taron na ranar litinin, an tattaro shi ne domin sulhunta shugabannin jam’iyyar biyu tare da baiwa jam’iyyar PDP tazarce a zaben shugaban kasa na 2023 da jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki.
Taron ya kuma samu halartar tsohon gwamnan jihar Ekiti kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Ayodele Fayose, da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP.