Kwamitin riko na jam’iyar APC ta kasa, ta cimma matsaya a kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar reshen jihar Kano.
A ranar Lahadi, 6 ga watan Fabrairu ne aka sake zama tsakanin bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau, bayan tattara bayanai da kwamitin ya yi, daga cikin matsayar da aka cimma shine cewa, dole ne kowane bangare ya yi aiki tare da dan uwansa, domin samun nasara.
Rahoton ya kuma kawo cewa kakakin Shekarau, Dr Sule Ya’u ya bayyana cewa an cimma matsaya, sai dai ya ce akwai karin bayanai da za a samu daga kwamitin a ranar Litinin.
Sule a hirar sa da BBC ya ce: “A batutuwan da aka gabatarwa bangarorin guda biyu akwai cewa jam’iyya ba ta sashi day aba ce, sannan kuma cewa ya zama dole kowani bangare ya tafi da dan uwansa don cimma nasara. Amma za a gabatar da cikakkun shawarwarin a ranar Litinin, kuma ana sa ran duka bangarorin biyu za su mika wuya ga wannan yarjejeniya wadda za ta samar da mafita a jihar.”
A nashi bangaren, tsohon shugaban Majalisar jihar Kano, Hon Kabiru Alhasan Rurum, wanda ke biyayya ga Gwamna Ganduje ya ce ga dukkan alamu komai ya zo karshe.
Rurum ya ce: “Muna da kyakkyawan zaton wannan lamar yazo karshe domin, uwa daya muke uba daya muke. “Abin da muke zaton ji maslaha daga kwamitin riko na wannan jam’iyya, saboda duka bangarorin mun yi wa juna wahala a baya.”