Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta bayyana dan takarar gwamnan jihar Cross River na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Cross River, Bassey Otu a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 18 ga watan Maris a shiyyar Kudu-maso-Kudu.
Otu wanda tsohon dan majalisar tarayya ne ya samu kuri’u 258,619 inda ya kayar da abokin hamayyarsa kuma dan takarar Sanata Sandy Onor na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) wanda ya samu kuri’u 179,636.
Karanta Wannan: Da Dumi-Dumi: APC ta lashe zaben gwamnan jihar Ebonyi
Da ayyana shi a matsayin zababben gwamna da alkalan zabe, Otu zai gaji gwamna mai ci kuma dan jam’iyyar APC, Ben Ayade wanda wa’adinsa na shekaru takwas zai kare a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Ya zuwa yanzu dai an bayyana sakamakon zaben gwamnoni 18. Jam’iyyar APC ce ke kan gaba da jihohi 12, PDP mai jihohi biyar sai kuma jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) mai jiha daya.