Kwamitin tantancewar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya kori mutane 10 da suka tsaya takarar shugabancin jam’iyyar.
Shugaban kwamitin, John Odigeie-Oyegun ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin da yake mika rahotonsa ga shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu.
Sai dai bai bayyana sunayen wadanda aka soke ba.
Kwamitin ya tantance ‘yan takarar shugaban kasa 23 a ranakun Litinin da Talata.
Wadanda aka tantance sun hada da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu; wani malami, Tunde Bakare; Gwamna Abubakar Badaru na Jigawa; tsohon gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun; tsohon gwamnan Zamfara, Sani Yerima da Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri.
Sauran sun hada da tsohon karamin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba; Felix Nicholas, fasto; mace daya tilo da ta tsaya takarar shugaban kasa, Uju Ken-Ohanenye; dan majalisar dattawa, Ajayi Boroffice; tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani da gwamna David Umahi na jihar Ebonyi. In ji Premium Times.
Gwamnan jihar Cross Rivers, Ben Ayade; Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan; Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi; Tein Jack-Rich; tsohon ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu; tsohon ministan yada labarai, Ikeobasi Mokelu; tsohon kakakin majalisar wakilai, Dimeji Bankole; Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi; Haka kuma an tantance tsohon ministan harkokin Neja Delta Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha.