Shugaban kwamitin tantance shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki kan zaben 2023, John Odigie-Oyegun, a ranar Juma’a ya ce, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba ya cikin wadanda aka tantance.
POLITICS NIGERIA ta ruwaito cewa, Oyegun a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan mika rahoton kwamitinsa na tantance masu neman shugabancin kasar nan a jam’iyyar APC, ya ce duk da cewa, wasu kungiyoyi sun saya wa Jonathan fom, tsohon shugaban na Najeriya bai kammala fom din ba, haka kuma ba a yi masa tambayoyi ba.
Jaridar ta ruwaito cewa kwamitin tantancewar na jam’iyyar APC a yau ya mika rahoton aikin ta ga shugabannin jam’iyyar.
An hana mutane 10 masu neman takara, amma har yanzu ba a bayyana sunayensu ba.
Jam’iyyar APC ta sayar da fom din tsayawa takara da shelanta sha’awa 28 na zaben shugaban kasa, inda 25 daga cikinsu suka cike suka koma jam’iyyar.
An shirya gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyya mai mulki a ranakun 6-8 ga watan Yuni.