An yi fargabar mutuwar mutane da dama tare da kona gidaje da shaguna da dama, bayan wata tankar mai ta fado daga bisani ta fashe a kusa da Ajegunle Bus-Stop kan titin Legas zuwa Abeokuta da misalin karfe 4 na safiyar Juma’a.
Politics Nigeria, ta rawaito cewa, wasu mazauna garin da ke diban mai da ke kwarara cikin magudanar ruwa sun afka cikin wuta.
Rahotanni daga kafafen yada labarai sun nuna cewa, a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021, Najeriya ta fuskanci mummunar gobara, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 79 daga cikin gobara 68 da aka samu cikin watanni 18.