An yi wa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo tiyata a kafarsa a yau, bayan kwantar da shi a asibiti da a ka yi.
Mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar Laole Akande ne ya bayyana haka a shafinsa na Twwiter.
Sanarwa ta ci gaba da cewa, mataimakin shugaban kasar ya ji raunin ne yayin wasan kwallon squash.
Nan gaba kadan ne a yau likitocin sa za su yi bayanin halin da yake ciki.