Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun yi garkuwa da wani jami’in sojan ruwan kasa a jihar Kogi.
Rahotanni sun bayyana cewa, a safiyar ranar Talata, sun ce jami’in sojan ruwa, Musa Lawal mai lambar yabo ta X12775 ABRP3 an yi garkuwa da shi ne a daren Litinin.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, jami’in da ke aiki da shelkwatar sojojin ruwa da ke Abuja, an dauke shi ne daga gidan sa da ke Lokoja da misalin karfe 8:00 na daren jiya.
An ce maharan sun lalata kofofin Lawal da tagoginsa kafin su shiga gidansa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Williams Ayah, wanda shi ma jaridar PUNCH ta tuntuba, ya ce har yanzu ba a sanar da hukumar faruwar lamarin ba, amma ya yi alkawarin jin ta bakin DPO din da abin ya shafa.