Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon babban sakataren hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, Ahmed Sani Toro.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ya tabbatar da sace mutanen a ranar Lahadi.
Wakili ya ce, ba shi da cikakken bayani kan lamarin kamar yadda ya faru a wajen jiharsa.
Ya ce: “Eh, labarin gaskiya ne. Na ci karo da daya daga cikin ‘ya’yansa, wanda ya shaida min cewa an sace shi ne a hanyar Akwanga a Nasarawa a lokacin da yake dawowa daga Abuja. Sauran bayanai idan na samu za a sanar da ku.”
Sai dai wani mai ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa a jihar Bauch, wanda kuma aminin Toro ne ya ce an sace tsohon mai taimaka wa NFF ne a daren ranar Asabar a hanyar Abuja zuwa Jos tare da wani tsohon mataimakin kocin Golden Eaglets, Garba Iliya.
Ya shaida wa Aminiya cewa dukkan mutanen biyu suna komawa Bauchi ne bayan halartar daurin auren dan tsohon shugaban Hukumar NFF, Alhaji Aminu Maigari a Abuja ranar Juma’a.
Majiyar ta ce, “Gaskiya an sace su ne a kusa da Ryom a Jihar Filato a lokacin da suke komawa Bauchi daga Abuja.