An yi garkuwa da matar shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin jihar Zamfara, Sanusi Mohammed Gusau.
Matar mai suna Ramatu Yunusa, an sace ta ne daga gidan mijinta da ke Damba Gusau da safiyar Talata.
Gusau wanda ya bayyana hakan ga jaridar The Punch, ya ce ‘yan bindigar sun shiga gidansa da misalin karfe daya na safiyar ranar Talata, inda suka yi awon gaba da matarsa mai ciki wadda za a haifo jaririn a kowane lokaci.
A cewarsa, yana farkawa ne a lokacin da ‘yan fashin suka tsallake shingen da nufin sace shi amma kwatsam ya buya inda ba su gan shi ba.
Gusau ya ce, “Sun tsallake bango suka karya min kofa amma kafin su shiga dakina na buya a wani wuri.
“Lokacin da suka binciki gidan ba su gan ni ba, sai suka sace matata mai ciki, Ramatu.”
“Tana iya haihuwa kowane lokaci daga yanzu saboda ranar da ake sa ran haihuwa a cikin wannan makon.”
Sai dai ya bayyana cewa har yanzu ‘yan bindigar ba su kai gare shi ba.