Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da yin garkuwa da Rev Father James Kantonma, limamin cocin Katolika na cocin St Anthony, Angware a karamar hukumar Jos ta Gabas a jihar Filato.
An ce an yi garkuwa da Father James, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a Jos ta Gabas a daren Lahadi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo, wanda ya tabbatarwa da SaharaReporters a ranar Litinin din da ta gabata, ya ce ana ci gaba da kokarin kubutar da limamin cocin ba tare da ya ji rauni ba.