fidelitybank

Da Dumi-Dumi: An yi garkuwa da daliban jami’ar tarayya ta Nasarawa

Date:

An yi garkuwa da wasu daliban jami’ar tarayya dake garin Lafia a jihar Nasarawa a kusa da harabar jami’ar.

Majiyar Daily Trust ta rwaito cewa, Majiyarmu ta bayyana cewa, an sace daliban ne a unguwar jami’ar da ke Maraba.

Jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Abubakar Ibrahim ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an sace dalibai hudu.

Ya ce, ‘yan bindigar sun far wa jama’ar jami’ar ne da misalin karfe 11:30 na ranar Alhamis inda su ka garzaya da daliban zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.

“Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Shehu Abdul Rahman, a madadin shugabannin hukumar, ya nuna matukar bacin ransa game da wannan abin takaici, ya kuma yi Allah wadai da shi da kakkausar murya da bukatar a gaggauta sakin wadanda aka sace.”

An jiyo mataimakin shugaban jami’ar na cewa, sace dalibai ya kasance daya daga cikin munanan matsalolin da ke barazana ga ilimi a jihar Nasarawa, musamman ma Najeriya baki daya.

Yayin da ya ke jajantawa iyalan daliban da aka sace, ya kuma tabbatar musu da cewa a na kokarin ganin an ceto wadanda lamarin ya shafa cikin gaggawa.

Sanarwar ta kara da cewa, “Mataimakin shugaban jami’ar, wanda tun lokacin da ya ziyarci yankin da aka yi garkuwa da daliban, ya ziyarci rundunar ‘yan sandan Nasarawa inda ya sanar da kwamishinan ‘yan sanda game da sace daliban.”

Rahotanni sun bayyana cewa, Farfesa Rahman ya bukaci daliban da su kara mai da hankali kan al’amuran da suka shafi tsaro, ya kuma yi kira gare su da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Ya yi nuni da cewa, an samar da karin matakan tabbatar da isassun tsaron rayuka da dukiyoyi a ciki da wajen Jami’ar.

sahara hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp