fidelitybank

Da Dumi-Dumi: An kuma kona ofishin INEC a jihar Imo

Date:

Kwanaki kadan bayan da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kona ofishin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a jihar Ebonyi, an kona wani wurin da hukumar ta ke.

Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a Festus Okoye ne ya bayyana hakan a ranar Lahadin da ta gabata.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Okoye ya ce, kwamishiniyar zabe ta jihar, Farfesa Sylvia Uchenna Agu, ta ruwaito lamarin da ya faru a karamar hukumar Oru ta Yamma yayin wani hari.

Ya ce, “Gaba daya, wannan shi ne karo na 7 da aka kai wa cibiyoyinmu a jihohi biyar na tarayya cikin watanni hudu da suka gabata.

“Har yanzu, hukumar ta nuna damuwarta kan sakamakon wani hari da aka kai wa cibiyoyinta a fadin kasar nan kan yadda ake gudanar da zabe musamman da kuma ayyukan zabe baki daya.”

Ya bayyana cewa an ja hankalin jami’an tsaro a jihar kan wannan lamari na baya-bayan nan domin gudanar da bincike.

legit latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

APC ta yi kwaf daya a zaben cike gurbin Kaduna da Jigawa

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi...

Ba mu yarda da zaben Ghari da Tsanyawa ba – NNPP

Jam'iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya...

QPC ta nemi INEC ta soke zaɓen Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zaɓen Kano: An kama Mutane 288 da tayar da zaune tsaye

Rudunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da kama mutum...

An Kama wakilin jam’iyya da Naira miliyan 25.9 na Siyan Kuri’a

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin...

Farashin kayan abinci na rugu-rugu a Najeriya – NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce hauhawar farashin...

Kotun Kano ta ce a kamo mata Dagacin Tamburawa

Kotun Shari’ar Musulunci da ke shelkwatar Hisbah a Kano,...

Kotu ta ƙwace motocin gwamnatin Zamfara guda 40 daga hannun Matawalle

Kotun Daukaka Kara da ke a Sokoto ta tabbatar...

A na cigaba da gudanar da zaben cike gurbi harda Kano

Kano na ɗaya daga cikin jhihohin da ake kaɗa...

Mutane 12 sun mutu a wani hatsari a Kano – FRSC

Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta...

Masarutar Rano ta haramta aurar da Yaran da ba su kammala karatun Firamare ba

Masarautar Rano a Kano ta haramta cire yarinya daga...

Matatar Dangote za ta fara jigilar mai kyauta ga gidajen mai

Matatar man Dangote za ta fara jigilar mai kyauta...
X whatsapp