Shelkwatar rundunar da ke Abuja ta nada sabbin kwamishinonin ‘yan sanda zuwa jihohin Kano, Zamfara da Enugu.
Kamar yadda ssanarwar ta ke a cewar Daily Nigerian ta ce, ‘yan sanda da aka tura Abubakar Lawal Kano, yayin da Yusuf Kolo aka tura jihar Zamfara.
Shi kuwa Ahmed Ammani an tura shi Enugu.
Sabon kwamishi nan na Kano, wanda aka yi masa canjin waje daga jihar Enugu, ya taba zama baturen ‘yan sanda DPO na Hotoro Kano.


