fidelitybank

Da Dumi-Dumi: An kashe Malamin makaranta tare da yin garkuwa da mutane 16 a Kaduna

Date:

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani malamin makaranta tare da wasu mutane hudu a hanyar Layin Lasan Tabanni a karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Rahotannin sun bayyana cewa an kuma yi garkuwa da mutane 16 a kauyukan Dogon Dawa, Layin Mahuta da Tabanni dake Gabashin karamar hukumar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Birnin Gwari Vanguard ya fitar mai kula da harkokin tsaro da kyakkyawan shugabanci mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar,

A cewarsu, a ranar 14 ga Maris, wasu ‘yan bindiga sun kashe Haruna Tanko Dogon Dawa da wasu biyu a hanyar Dogon Dawa zuwa Zariya.

“An yi garkuwa da wasu mutane takwas a hanya daya. A Layin Mahuta (Tabanni) an kashe wani Abdullahi Abubakar malamin makaranta a kan hanyar Layin Lasan Tabanni ranar Laraba 16 ga Maris 2022. Yayin da a ranar Alhamis 17 ga wata, an kuma kashe wata tsohuwa mai shekaru 70 tare da sace mata bakwai a Layin Mahuta Tabanni. An sace wasu mutane biyu a tsohon Tabanni,” Ibrahim Abubakar Nagwari.”

Shugaban ya kara da cewa a yankin Randagi ‘yan bindiga sun sako mutane 32 daga cikin 46 da aka yi garkuwa da su a Unguwar Bula da Ijinga makonni uku da suka gabata bayan sun biya Naira miliyan 16 kudin fansa.

Kungiyar ta kuma bukaci jami’an tsaro da su rika amsa kiraye-kirayen kai daukin gaggawa a unguwannin Dogon Dawa, Kuyello, Tabanni, da Kutemashi a cikin Birnin Gwari.

sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp