A ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka kashe DPO, Mukhtar Sabiu da wasu mutane hudu a garin Paiko, hedikwatar karamar hukumar Paikoro ta jihar Neja.
Wani mazaunin yankin mai suna Musa Idris wanda ya ce da kyar ya tsere, ya ce an harbe wadanda aka kashen ne a kauyen Kwakuti da ke kan hanyar Minna zuwa Suleja ranar Asabar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya ce an kashe DPO da mutanen sa ne a wani artabu da bindiga.
Ya ce rundunar ta samu bayanai da misalin karfe 1100 na sa’o’i, cewa an ga ‘yan bindiga dauke da makamai a kusa da kauyukan Kwakuti-Dajigbe na Lambata, a kokarinsu na kai farmaki kan wasu al’ummomin da ke kusa da karamar hukumar Gurara.
Hedikwatar ‘yan sanda ta kasa ta tattara tawagar jami’ai da maza daga Dibishin Gawu-Babangida da na Paiko; An kuma shirya jami’an soji da na ‘yan banga zuwa wurin.
Ya ce ‘yan sandan sun yi musu artabu da bindiga tare da dakile harin inda aka kashe da dama daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbin bindiga.