An kashe akalla mutane uku da ake zargin barayin siyasa ne a karamar hukumar Gboko da ke jihar Benue.
DAILY POST ta tattaro cewa yan barandan sun mamaye rumfunan zabe na 026 da 004 dake Gboko ta kudu yayin da ake ci gaba da gudanar da zabe tare da yunkurin kwace akwatunan zabe da kuma Bimodal Voters Accreditation System, BVAS.
Wani ganau mai suna Moses Agure-Dam wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar DAILY POST, ya ce jami’an soji ne suka bindige ‘yan barandan.
Karanta Wannan:Â An samu rahotannin siyen kuri’u a Kano
Ya ce, “’yan barandan sun mamaye rumfunan zabe inda suka hargitsa zaben. Su uku ne, daya ya kwace BVAS yayin da wasu suka kwace akwatunan zabe amma ba su yi nasara ba.
“Sojoji a yankin ne suka harbe su gaba daya.”
Kokarin da DAILY POST ta yi na jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Binuwai, DSP Catherine Anene ya ci tura saboda ba a iya samun lambarta.