Jami’an bayar da agajin gaggawa, sun gano gawar wani mutum mai shekaru 52 da haihuwa da kuma mace ‘yar shekara 20 da ake kyautata zaton hatsarin kwale-kwale ne ya rutsa da su a Legas.
Ibrahim Farinloye, Ko’odinetan shiyyar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) na shiyyar Kudu-maso-Yamma, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na NAN a ranar Asabar a Legas.
Farinloye ya ce, lamarin ya faru ne sakamakon wani jirgin ruwan Fiber na fasinja na W19 dauke da mutane 16 da ya kife a yankin Ojo da ke jihar.
Ya ce kwale-kwalen da ya taso daga Mile 2 zuwa Ibeshe a yankin Ojo, ya kife ne a lokacin da yake gudanar da aiki da daddare, wanda ya saba wa ka’idar hanyar ruwa.
Farinloye ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7.45 na yammacin ranar Juma’a.