Wani ginin ya rushe a Abuja, kuma akwai fargaba baraguzan ginin sun danne mutane masu yawa.
Wasu wadanada suka shaida lamarin sun ce ana cikin hada ginin ne, ba a kammala shi ba ma. Iftila’in ya auku ne a Gwarinpa a ranar Alhamis. In ji BBC.
Karanta Wannan: Jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya fara aiki
Wani mutum a Tiwita mai suna @nnjigs ya wallafa bidiyon ginin kuma cikin sakonsa na Tiwita, ya yi ikirarin akwai mutanen da baraguzan ginin suka danne:
“Yanzu na ga wannan ginin ya ruguje a filin da ake gina shi a daidai layi 4th Avenue. Akwai mutane a karkashin baraguzan gini. A taimaka a sanar da dukkan hukumomin da lamarin ya shafa.”