Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya sanar da dakatar da haƙar ma’adinai a Ƙananan Hukumomin Shiroro da Munya da Rafi.
Gwamnan ya bayyana haka ne biyo bayan harin da ƴan bindiga suka kai wani wurin haƙar ma’adinai da ke ƙauyen Ajata Aboki da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke jihar.
A cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane ya fitar, sakataren ya ce akwai buƙatar a dakatar da haƙar ma’adinai sakamakon yadda rashin tsaro ke ƙara ƙamari ƴan kwanakin nan.
Ya ce sun lura da cewa wuraren haƙar ma’adinan na jawo masu aikata laifuka waɗanda suke kasancewa barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kuma yi gargaɗin cewa duk waɗanda aka kama suna gudanar da ayyukan haƙar ma’adinai za su yaba wa aya zaƙinta