Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari, tare da wasu mutane shida da ake zargi da safarar hodar iblis, sun isa babbar kotun tarayya da ke Abuja, gabanin gurfanar da su gaban kuliya a yau Litinin.
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, a ranar 28 ga watan Fabrairu, ta shigar da kara kan laifuka takwas da suka shafi mu’amala da hodar iblis ba bisa ka’ida ba.
Jami’an NDLEA sun gurfanar da Kyari tare da wadanda ake zargin sa kotu da karfe 8:12 na safe a cikin wata motar Black Hiace a ranar Litinin.
Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kuma zargi Kyari, a wani kidaya da ya nuna shi kadai a matsayin wanda ake tuhuma, da yunkurin kawo cikas ga hukumar ta NDLEA da jami’anta ta hanyar bayar da dala 61,400 ga wani babban jami’in yaki da safarar miyagun kwayoyi a matsayin wani yunkuri na hana gudanar da gwajin kilo 17.55 na hodar iblis.
A cewar NDLEA, hudu daga cikin wadanda ake tuhumar Kyari jami’an ‘yan sanda ne na rundunar ‘yan sanda ta Intelligence Response Team (IRT) da ke karkashin jagorancinsa har sai da aka dakatar da shi sakamakon tuhumar da aka yi masa a Amurka a shekarar da ta gabata.
Jami’an IRT hudu da ake tuhuma tare da Mista Kyari su ne — Sunday J. Ubua, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda; Bawa James, mataimakin sufeton ‘yan sanda; Simon Agirgba, sifeto; John Nuhu, shima sifeto.
Sauran wadanda ake tuhumar sun hada da Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne.
Hukumomin Amurka a shekarar da ta gabata sun saka sunan Mista Kyari cikin wasu mutane biyar da ake zargi da hada baki da Ramon Abass aka Huspuppi, wani shahararren Instagram, a cikin damfarar dala miliyan 1.1 da aka yi wa wani dan kasuwa dan kasar Qatar.