fidelitybank

Da Dumi-Dumi: A na zanga-zanga a Sokoto

Date:

Zanga-zanga ta ɓarke a garin Sokoto, inda matasa ke ci gaba da nuna ɓacin ransu kan kalaman ɓatanci da ya jawo kisan wata matashiyar ɗaliba mai suna Deborah Samuel.

Masu zanga-zangar na neman jami’an tsaro su saki mutanen da suka kama da ake zargi da kisan matashiyar da ke karatu a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, wadda suka zarga da zagin Annabi Muhammadu (SWA).

Matasan maza da mata suna aiwtar da zanga-zangar a wurare daban-daban a fadin Sokoto tare da ƙona tayoyi, da suka haɗa da Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III. Kazalika wasu sun yi cincirundo a ƙofar gidan gwamnatin jihar.

Rahotannin da BBC ta samu sun nuna cewa da farko zanga-zangar ta lumana ce, daga bisani sai ta rikide ta zuwa tamkar rikici, inda mutane suka dinga jefa duwatsu kan gidan sarkin Musulmin.

Wani da BBC ta zanta da shi da ke kusa da fadar sarkin a lokacin da abin ya faru ya ce jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin dakatar da matasan kutsawa fadar.

“Da yawa yaran (‘yan zanga-zanga) na ganin sarkin ya goyi bayan yarinyar (Deborah), shi ne suke jefe-jefe,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na ‘yan sanda da soja sun harba hayaƙi mai sa hawaye, har ma an harbi mutum biyu.

legitnews.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp