A na fargabar mutuwar mutane da dama, sakamakon fashewar wani bututun man fetur.
Lamarin ya faru ne da safiyar Juma’a a Rumuekpe da ke karkashin karamar hukumar Emohua a jihar Rivers.
Adadin wadanda suka mutun dai ana hasashen ya zarce goma sha biyu, ko da yake babu wani tabbaci a hukumance kamar dai lokacin da aka buga labarin.
Bayanan da ake samu sun nuna cewa fashewar, wacce kuma ta cinye ababan hawa, ta taso ne daga wurin bututun mai.
Wani direba ya loda daya daga cikin motocin bas din a wurin dauke da danyen mai a cikin jarkuna.
Yana shirin kwashe kayan man fetur daga wurin, ya kunna injin motar wanda ya haifar da fashewar.
Mutumin da wasu da ke kusa da su na cikin wadanda suka mutu.