A na bikin rantsar da sabbin zababbun mambobin kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar APC mai mulki a Abuja.
A karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu, mambobin kungiyar ta NWC sun yi rantsuwar kama aiki tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da shugabanni da mambobin jam’iyyar da suka halarta.
Shugaban kwamitin gudanar da babban taron, Gwamna Badaru Abubakar, ya ce, daga cikin ofisoshi 36, guda biyar ne kawai aka fafata a yayin da sauran kuma suka kasance ta hanyar amincewa.