Gabanin zabukan 2023, Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Sanata Chris Ngige a ranar Talata ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a hukumance.
Ya na mai cewa, yana da muradin ganin Najeriya ta samu ci gaba, hadin kai da daidaito.
Ngige, wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a gaban dimbin jama’a a cocin St. Mary’s Catholic Church Alor, da ke karamar hukumar Idemili ta Kudu a jihar Anambra, yana neman tikitin jam’iyyarsa ta APC a matsayin dan takararta na shugaban kasa.
A jawabin da ya yi wa taron wanda ya kunshi amintattun jam’iyyar APC da sauran magoya bayansa, tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce ya shafe shekaru 40 yana aikin gwamnati, ya samu cikakken kayan aiki a matsayin mai gudanar da mulki, yana da dimbin kwarewa, iya aiki da kuzari da kuma zuciya mai tarin yawa. don daidaita bambance-bambancen da ke tsakanin ‘yan Najeriya.