Shugaba Muhammadu Buhari, ya umarci jami’an tsaro su sake jajircewa wajen ceto sauran fasinjojin jirgin kasa da aka yi garkuwa da su a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban ya ce, ya yi farin ciki fasinjojin da aka sako, kuma za a ci gaba da kokari wajen ganin sauran mutanen da ke hannun ‘yan bindiga sun dawo gida cikin koshin lafiya.
Wannan dai na zuwa ne tun bayan da mai ganawa a tsakanin juna da ‘yan ta’addan, ya bayyana cewa, rayuwar sauran mutanen na cikin hadari.