Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar Talata ya bayar da belin dan takarar shugaban kasa kuma tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha.
Okorocha, an bayar da belinsa a kan kudi Naira miliyan 500 da kuma wanda zai tsaya masa.
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ne ta gurfanar da shi a gaban kotu sakamakon zarginsa da damfarar Naira biliyan 2.9.
Mai shari’a Ekwo ya bayar da umarnin cewa wanda zai tsaya masa dole ne ya kasance dan kasa mai cikakken iko wanda ya mallaki dukiya a cikin kwatankwacin adadin belin da aka bayar Okorocha.
Haka kuma, Mai shari’a Ekwo ya hana Sanatan fita Najeriya sai dai da izinin kotu.
A halin da ake ciki kuma ana sa ran Okorocha zai ci gaba da kasancewa a hannun hukumar EFCC har sai an cika sharuddan belin sa.