Hukumar ‘yan sandan farin kaya (DSS), ta kama Jeremiah Oluwaferanmi, wani ma’aikacin cibiyar binciken ‘yan jarida ta Premium Times (PTCIJ) a zaben gwamnan Ekiti da ke gudana.
A cewar wani abokin aikinsa da ya zanta da Nairametrics, an kama shi ne a Ward 1 Unit 1, a ƙaramar hukumar Irepodun Ifelodun, yankin zaben tsohon gwamnan, Ayodele Fayose.
Kamar yadda takwarorinsa suka bayyana, jami’an DSS sun isa rumfar zaben suna tambayar wanene ya saka hoton bidiyo na sashin zaben shafin intanet kafin suka tafi da shi cikin motar.
Mista Omoniyi wanda dalibi ne na Jami’ar Jihar Ekiti yana tsare a ofishin ‘yan sanda na Iworoko a cewar wata majiya.