Shahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil ya fito takarar gwamna a jam’iyyar ADC a jihar Kano.
Solacebase ta ruwaito cewa, Sheikh Khalil, wanda ya fito ba tare da hamayya ba a matsayin dan takara a yayin wani buki na musamman a ranar Lahadin da ta gabata, zai fafata da ‘yan takarar jam’iyyun siyasa mafi rinjaye a Kano.
A yayin da yake mika wa Sheikh Khalil fom din tsayawa takarar gwamna a jam’iyyar ADC a gidan Mumbayya da ke Kano, shugaban jam’iyyar na kasa, Cif Ralph Okay Nwosu ya bayyana cewa, an tabbatar da Sheikh Khalil zai rike tutar jam’iyyar ADC a zaben gwamna na shekara mai zuwa saboda rikon amana.
Shugaban jam’iyyar na kasa wanda ya bayyana gaskiyar jam’iyyar a kan gaskiya da mutunci, ya jaddada cewa, Sheikh Khalil ya kwatanta cancantar da ADC za ta kwato Kano. A cewar Solacebase.