Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta kammala cinikin ɗan wasan tsakiya na ƙasar Ukraine, Oleksandr Zinchenko, daga Manchester City.
Zinchenko wanda ya buga wasanni da dama a ɓangaren hagu na bayan Man City, wasa 15 kawai ya buga a kakar wasan da ta gabata a yunƙurin ƙungiyar na kare kambin Premier League da ta ɗauka.
Ɗan ƙwallon mai shekara 25 ya je Arsenal ne daga zagayen da City ke yi a Amurka don kammala komawarsa tasa bayan Arsenal ta amince da yarjejeniyar da ta kai fan miliyan 30.
Shi ne ɗan wasa na biyu da yake komawa Arsenal daga City a bazarar nan.
Tuni Gabriel Jesus ya koma Emirates kan fan miliyan 45, inda har ma ya ci mata ƙwallo wasan sada zumunta. In ji BBC.