Dan majalisar mai wakiltar Jalingo, Yorro, Zing a jihar Taraba, Ismaila Yushau Maihanchi ya rasu.
Rasuwar tasa, ta faru ne da sanyin safiyar ranar Asabar a babban birnin tarayya, Abuja.
Da yake tabbatar da rahoton, kakakin jam’iyyar PDP, Andeta’rang Irammae, ya ce jim kadan bayan zaben, zababben dan majalisar ya kamu da rashin lafiya kuma yana jinya a Abuja.
Da yake bayyana rasuwarsa a matsayin rashin sa ga jam’iyyarsa, ya ce marigayin ba jam’iyyar kadai za ta yi kewar sa ba, har ma al’ummar jihar baki daya.
Shi ma da yake jawabi, mukaddashin shugaban jam’iyyar, Abubakar Bawa, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rauni ga iyalan PDP a jihar da ma kasa baki daya.
Majiyar dangin ta ce za a sanar da shirye-shiryen jana’izar daga baya.
Zababben dan majalisar da ya fafata a zaben majalisar dokoki ta kasa a karkashin jam’iyyar PDP, ya doke abokan hamayyarsa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, New Nigerian Peoples Party, NNPP da Social Democratic Party, SDP da gagarumin rinjaye.


