Ana ci gaba da damawa gabanin zaben 2023 yayin da Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike ya ce, ya bar Turkiyya zuwa Faransa, domin ganawa da dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.
Makusancin Tinubu kuma mai ba Gwamnan Jihar Legas shawara na musamman kan Muhalli da Ruwa, Joe Igbokwe ne ya bayyana hakan a ranar Laraba.
Igbokwe ya ce, yayin da suke cikin shafukan sada zumunta suna cin zarafin kowa, Wike ya tafi Faransa don ganawa da Tinubu.
Ya bayyana a shafin sa na Facebook cewa: “A yayin da suke cikin kafafen sada zumunta na zamani suna cin zarafin duk wani Gov Wike ya je Faransa don ganawa da Asiwaju. Zagi, kiran suna, ƙiyayya da son zuciya ba dabara ba ne.
“Sun tsani Buhari da cin zarafi tun 2015 kuma yanzu sun mayar da ta’addancin ga Asiwaju. Muna jira mu gani.”
Wike dai ya sha takun saka da PDP tun bayan da Atiku Abubakar ya rasa tikitin takarar shugaban kasa.
Atiku ya yi watsi da Wike lokacin da ya zabi Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta a matsayin abokin takararsa.