Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya fita kasar waje da sanyin safiyar ranar Litinin, bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa.
Ya tafi zuwa Paris, Faransa. don gudanar da wasu muhimman taruka.
Ana sa ran dan takarar jam’iyyar APC zai dawo kasar nan ba da jimawa ba.
Kafin tafiyarsa, ya halarci taron baje kolin wani littafi mai suna ‘Mr. Kakakin Majalisa da kaddamar da shirin nasiha na majalisa don tunawa da cika shekaru 60 na shugaban majalisar Femi Gbajabiamila.