Shugaban kasa, Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar baiwa ɗalibai lamuni.
Wani mai taimaka wa shugaban kasa, Dele Alake ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar shugaban kasa da yammacin ranar Litinin.
Kudirin dai zai baiwa daliban Najeriya damar samun lamuni a farashi maras riba.
Ku tuna cewa dokar ta tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai a ranar 25 ga Mayu, 2023.


