Jagoran jam’iyyar APC kuma ɗan takara a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ke kan gaba da yawan kuri’u aka soma kidayawa, domin tantace yawan kuri’un da kowanne ɗan takara ya samu.
Sauran wadanda suka samu kuri’a a wannan tantacewa sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, tsohon ministan Rotimi Amaechi da gwamnan Kogi, Yahaya Bello.
Ana dai kan tantace kuri’un da daliget 2,340 suka kada.
Da misalin karfe 2:40 na daren jiya aka soma zaɓe har zuwa 8 na safen yau Laraba.