Omoyele Sowore, dan rajin kare hakkin dan Adam kuma mawallafi, ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC).
A ranar Alhamis ne jam’iyyar AAC ta gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa a Abuja. A nan, wakilai sun yi amfani da kada kuri’a daidai da dokokin zabe tare da tabbatar da Mista Sowore a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Nasarar da ya yi a yau ta tabbatar Mista Sowore ya zama ɗan takarar shugaban kasa a karo na biyu. Ya kasance dan takarar jam’iyyar a 2019.
Mista Sowore ya samu kuri’u 33,953 a rumfunan zabe, a kan ‘yan adawa kamar Fela Durotoye na jam’iyyar Alliance for New Nigeria (ANN) da Kingsley Moghalu na jam’iyyar Young Democratic Party (YPP).