Rundunar sojin Najeriya a ranar Talata ta ce, ta kama wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne da suka kai hari a cocin St. Francis Catholic Church, Owo, jihar Ondo.
Sama da masu ibada 40 ne aka kashe a ranar 5 ga Yuni, 2022 lokacin da ‘yan ta’adda suka mamaye cocin a lokacin hidimar Mass kuma suka bude wuta kan masu ibada.
Harin ya janyo tofin Allah tsine da bacin rai a duniya.
Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a hedikwatar tsaro da ke Abuja.
Ya ce, an kama masu laifin ne tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro, kamar yadda jaridar Nation ta ruwaito.