Ƙasar Senegal ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afrika a karo na farko a hannun Masar.
Senegal ta samu nasara a bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan da a ka shafe mintuna 120 a na fafatawa a fili.
Ƴan wasan Masar biyu sun zubar da bugun su, yayin da ɗan Senegal ɗaya ya zubar da ta sa, daga bisani mai tsaron raga Mendy ya ƙara buge ɗaya wanda abkantashin4-2.
Yayin wasan mai tsaron raga Gabaski na Masar ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasa na gasar, sai Mendy gwarzon ɗan wasa na Continental.
Shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya, shi ne ya miƙa kofin fa Senegal, bayan da shugaban hukumar ƙwallon ƙafa na duniya, Gianni Infantino, ya miƙa masa kofin.