Ƙasar Rasha ta harba makamai biyu masu linzame a yankin Kudu maso Yammacin birnin Kiev na ƙasar Ukraine da safiyar Asabar ɗin nan.
kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya rawaito cewa, hukumomin birnin sun ce, ɗaya daga cikin harin ya shafi wani dogon gini na rukunin gidaje.
Haka zalika, ɗaya daga cikin harin ya shafi yankin da ke kusa da filin jirgin sama na Zhuliany na Ukraine.