Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Suleman Sabo na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban karamar hukumar Kuje da aka gudanar a babban birnin tarayya Abuja ranar 12 ga watan Fabrairu.
Suleman Sabo, shugaban karamar hukumar wanda a yanzu zai yi wa’adi na biyu a kan karagar mulki, ya doke sauran ‘yan takara biyar a kowace shiyya 10 na karamar hukumar.
Ya tattara jimillar kuri’u 13,301 inda ya kayar da abokin hamayyarsa, Sarki Hamidu na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 7,694 ya zo na biyu.
Da wannan ne dan takarar PDP ya doke APC da kuri’u 5,607.
Sule Magaji jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a zaben karamar hukumar Kuje ne ya sanar da sakamakon zaben da safiyar Lahadi.
An sanar da sakamakon gundumomi a hukumance:
Kuje Central (ward 01)
APC- 1717
PDP-3671
Chibiri (ward 02)
NIRSAL AD
APC- 1,172
PDP–1,839
Gaube (ward 03)
APC – 1793
PDP -2,226
Kwaku (ward 04)
APC :562
PDP: 1450
Kabi (ward 05)
APC- 271
PDP-433
Rubochi (ward 06)
APC – 1047
Tallace-tallace
PDP – 1506
Gwargwada (ward 07)
APC- 365
PDP-583
Gudrun Karya ( ward 08)
APC -420
PDP -1032
Kujekwa (ward 09)
APC-76
PDP:106
Yenche (ward 10)
APC:271
PDP: 455