Hukumar NDLEA ta kama wasu mutane bakwai da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano a watan Mayu da Yuni
Kwamandan NDLEA a filin tashi da saukar jiragen sama, Sani Abubakar, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Kano, a bikin tunawa da ranar yaki da fataucin miyagun kwayoyi na Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 2022.
Ya kuma bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin ne dauke da hemp na Indiya, tramadol, pentazocine da kuma khaat da dai sauransu kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su a gaban kuliya.
“An kama su ne a filin jirgin yayin da suke kokarin shigo da kwayoyi cikin kasar nan. Kimanin kilogiram 470.21 na kwayoyi an kwace daga hannun wadanda ake zargin,” in ji jami’in NDLEA. Jami’an NDLEA sun kuduri aniyar dakile yunkurin amfani da filin jirgin sama don safarar miyagun kwayoyi.
Malam Abubakar ya kuma kara da cewa karin ma’aikata, samar da kayan aiki da kuma kyautata jin dadin ma’aikata sun taimaka wajen ci gaban da hukumar NDLEA ke samu.