Wata motar dakon man fetur ta kama da wuta yayin da take sauke man fetur a Kano.
Lamarin ya faru ne da wajen ƙarfe 8:30 na dare a wani gidan mai na Mumin dake kusa da gadar sama ta Kabuga.
Yayin haɗa wannan rahoton, shaidun gani sun tabbatar wa da Platinum Post Hausa cewa, kawo lokacin motar na ci ganga-ganga.
Tuni dai hukumar kashe gobara ta kai ɗauki wajen domin kashe wutar.