Manyan ministocin Birtaniya biyu sun yi murabus sakamakon ce-ce-ku-cen da ake yi kan Firaiminista Boris Johnson.
Ministan kuɗi Rishi Sunak da Ministan Lafiya Sajid Javed duka sun bayar da takardar ajiye aikinsu – lamarin ya jawo matsin lamba matuƙa kan Firaiminista Boris Johnson.
Ana zargin Boris Johnson da yin kalamai da dama masu cin karo da juna. Ko a kwanakin baya sai da aka yi ƙuri’ar raba gardama kan Mista Johnson ɗin. A cewar BBC.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ministan lafiya Sajid Javed ya wallafa takardar ajiye aikinsa inda ya ce ya yi magana da faraiminista domin ya yi murabus.