fidelitybank

Da Ɗumi-Ɗumi: Ministoci 10 na Buhari sun yi murabus

Date:

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi ban-kwana da ministocinsa da suka ajiye aiki don yin takara a babban zaɓe mai zuwa na 2023.

Yayin jawabinsa a ranar Juma’a, Buhari ya ce ya yi imani da yawa daga cikin ministocin na da ƙwarewar da za su iya gadarsa.

“Babu wata tantama idan aka samu shugaban ƙasa daga cikin ministocin nan za a ga cikakkiyar ƙwarewa da kuma tsabar aiki ga al’umma,” in ji shi.

“Wannan na ɗaya daga cikin tarihin da za mu bar wa ‘yan Najeriya.”

A ranar Laraba ne Shugaba Buhari ya umarci dukkan ministoci da shugabannin hukumomi da ma’aikatu masu son tsayawa takara a muƙamai daban-daban da su ajiye ayyukansu nan da ranar Litinin mai zuwa.

Daga cikin ministocin da suka yi ban-kwana da shugaban a ranar Juma’a har da Ministan Shari’a Abubakar Malami, wanda rahotanni ke cewa zai yi takarar gwamna a jiharsa ta Kebbi.

Ministocin su ne:

  • Ministan Shari’a Abubakar Malami
  • Ministan Sufuri Rotimi Amaechi
  • Ministan Ƙwadago Chris Ngige
  • Ƙaramin Ministan Man Fetur Timpre Sylva
  • Ministan Neja Delta Godswill Akpabio
  • Ministan Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu
  • Ministar Harkokin Mata Pauline Tallen
  • Ƙaramin Ministan Ma’adanai, Uche Ogah
  • Ministan Kimiyya da Fasaha Ogbonnaya Onu
  • Ƙaramin Ministan Neja Delta Tayo Alasoadura.

Shugaba Buhari wanda ya ɗare mulki a 2015 zai kammala wa’adin mulkinsa nea watan Mayun 2023, yayin da za a yi zaɓukan ƙasar kuma a Fabrairun 2023.

Ana sa rana jam’iyyun siyasa za su gudanar da zaɓukan fitar da gwani kafin ranar 3 ga watan Yunin 2022. In ji BBC.

nigerianewstoday

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp