An yi garkuwa da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba a Abuja, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a cikin gidajensu da sanyin safiyar ranar Litinin.
Gidan da aka kai harin yana unguwar Gwarinpa ne a Abuja, babban birnin tarayya, inji rahoton Naija News Hausa.
‘Yan bindigar wadanda aka ce sun zo ne da wasu makamai da suka hada da baka, kibau, da adduna, sun gudanar da aikin ne a yankin tsakanin karfe daya na safe zuwa karfe hudu na safe.
Da yake bayyana hakan, wani mazaunin garin mai suna Mohammed ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa, ‘yan bindigar sun samu shiga Estate ne, bayan Efab Queens da ke 6th Avenue, Gwarinpa.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Josephine Adeh, ta bayyana faruwar lamarin a matsayin na fashi da makami ba wai na garkuwa da mutane ba.
Ta kara da cewa, an tattara jami’an ‘yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru tare da yin alkawarin bayyana sakamakon binciken su ga jama’a da zarar an samu karin haske.