fidelitybank

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar dokokin Kano za ta binciki Pillars

Date:

Majalisar dokokin jihar Kano, ta umurci kwamitinta na kula da harkokin wasanni da ya binciki ficewar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars daga gasar kwallon kafa ta Najeriya NPFL.

Hakan ya biyo bayan amincewa da kudirin mahimmancin jama’a da Alhaji Nurudeen Alhassan (APC-Rano) ya gabatar yayin zaman majalisar na ranar Litinin a Kano.

Da yake gabatar da kudirin, Alhassan, kuma shugaban kwamitin riko na majalisar, ya bayyana wasanni a matsayin ginshikin ci gaban matasa.

A cewarsa, ficewar Kano Pillars daga NPFL wani lamari ne mai ban tausayi wanda dole ne a yi bincike sosai don hana afkuwar lamarin nan gaba.

Majalisar ta amince da kudirin baki daya, sannan ta bukaci kwamitin da ke kula da harkokin wasanni da ya gudanar da bincike tare da bayar da rahoto cikin makonni biyu domin ci gaba da aiwatar da dokar.

legit news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Bayan kashe Soja yanzu haka an kama ƴan Daba 398 a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna, ta sanar da kama...

Shettima zai san makomarsa bayan taron APC na ƙasa – Fadar Shugaban Ƙasa

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa, sai bayan babban...

Kotu ta ɗaure Matashin da ya shiga ɗakin kwanan Ɗalibai Mata a Kano

Babbar Kotun Shariʼar Musulunci da ke Kofar Kudu a...

Ban gudu daga PDP ba – Namadi Sambo

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Mohammed Namadi Sambo, ya ƙaryata...

Da yuwar Sojojin mu za su shiga yaƙi don tallafa wa Isra’ila – Trump

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta ce ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta kai hari cibiyoyin ƙera nukiliyar Iran

Yayin da aka shiga rana ta shida na yaƙi...

Najeriya za ta kwashe ƴan ƙasarta dake zaune a Iran da Isra’ila

Gwamnatin tarayya ta ce, tana kammala shirye-shiryen gaggawa domin...

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...
X whatsapp