Majalisar Wakilai ta tarayya ta amince da ƙudirin ƙara wa’adin kasafin kuɗin ƙasar da wata biyu.
A zamanta na yau, majalisar ta yi wa Dokar Kasafin Kuɗi ta 2021 kwaskwarima, inda aka sauya wa’adin ƙarewar dokar daga 31 ga watan Maris 2022 zuwa 31 ga Mayun 2022.
Majalisar ta ce, ta ɗauki matakin ne bayan kwamatinta ya je zagayen ganin ayyuka kuma shi ne ya ba da shawarar ƙara wa’adin don samun gudanar da ayyukan a cikin dokar ta 2021.