Wani jami’in hukumar kwallon kafar Afirka Dr. Joseph Kabungo ya mutu ‘yan mintoci kadan bayan Black Stars ta Ghana ta fitar da Najeriya daga samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2022 a filin wasa na Moshood Abiola na kasa da ke Abuja a ranar Talata.
Dr. Kabungo ya kasance likita dan kasar Zambia. Rahotanni sun bayyana cewa, ya rasu ne sakamakon turmutsitsin da ya faru a filin wasan bayan da magoya bayansa suka mamaye filin wasan bayan kammala wasan.
Wani dan jaridan Najeriya na kasar Birtaniya, Osasu Obayiuwana, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, an tabbatar da mutuwar likitan ne bayan an garzaya da shi asibiti.