Kimanin jami’an rundunar sojin Najeriya akalla hudu da ke da hannu a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabas ne wata kotun Soji ta musamman suka kafa suka ba da shawarar korarsu daga aiki.
Har ila yau, an ba da shawarar a daure wasu 30 a gidan yari.
Kwamandan Operation Hadin Kai, Manjo Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa, an gabatar da jimillar sojoji 227 a gaban kotun.
Ya kara da cewa, babban kotun soji da na musamman ya kuma ba da shawarar ma’aikata 25 da za a rage musu girma, 20 a yi hasarar albashi da kuma wasu 17 da su fuskanci tsangwama.